MU'AMALAR UWA DA JARIRINTA
JARIRIN DAKE CIKIN BACCI
Yayin da zaki tashi jaririnki daga bacci musamman danyin wanka karki jijjigasa, karkuma ki debosa ki danna aruwan zafi kamar yadda ake saide inyaji dumi ya bude ido. Abunda zaki kurum rika hura iskar bakinki a tsakiyar kansa wannan itace kyakkyawar hanyar farkar dasu.
BAYAN JARIRI YA FARKO BACCI
Idan yaronki ya farko daga bacci musamman cikin kuka wasu kokarin bashi ruwa suke fara yi kafin daga bisani asashi a nono. Wannan kuskure ne. Nono zaki fara dorasa yasha sanda ya farko cikin bacci. Bashi ruwa irin wannan lokacin kan jawo musu zawo da kankancewa.
YA ZAN GANE YANA JIN YUNWA ?
Idan kikaga jaririnki yana yawan Qwalla wato hawaye na yawan kwaranyowa daga idanunsa batare da kuka yake ba; Toh alama ce ta nono baya isar jaririnki wannan shine alamar dake miki nuni domin ba baki garesa ballantana.
Don haka musamman mata masu haihuwar fari baku cika Kän gadon fahimtar haka ba, wani lokacin harma da wadanda suka dade suna haihuwar don haka asa ido akula, a tabbatar ana samun ingantacciyar shayarwa.
TA YA ZAN GANE JARIRINA YA KOSHI TOH ?
Daga lokacin da kika ga jaririnki yana cillo fitsari abunsa, nan da nan sai aji malalo fitsari abunsa toh wannan alama ce ta nono na isarsa, ma'ana yawan fitsarin jariri shike nuni da ingantacciyar shayarwa.
ME ZAI TAIMAKA MUN YARON YA ZAM YA KOSHI ?
Eh wasu kanyi kuskure idan nono ya subuce daga bakin Yaro sai su dauka kurum ya koshi ne, ko kuma ta kosa tai wani abu don haka koya ya Jima sai kaga uwa ta janye nono ta tashi inde ba kuka taji ya saka ba,
Don haka duk macen dake haihuwa ta Sani Yaro Kän Jima ne yana tsotso karshenta dalilina baki hadashi da jikinki ya kama nonon sosai ba, don haka kadan yake zuwa shyasa yake d'ad'ewa kuma kike Jin zafi domin Kän kurum kike dosana masa, uwa uba irin wannan shiriritar shayarwar kesa cikin Yaro kumbura saboda iskar da yake zuqa hade da nono, wannan kesa wani jaririn yaita kuka, ko aga yai kwanaki ba kashi.
Don haka ki zauna guri guda ki nutsu, kike kuma goge Kän nononki duk sanda ya gama sha da ruwa, karkurum ki jawo bra ki saki anjima kuma ki kara daga masa ki cusa bakinsa hakan zaisa yaji karnin da zai hana sa kamawa ko kuma bacteria din fatarki ta nishi gurin yaronki ya tsotsa ya kama gudawa duk ya lalace kankanin lokaci.
Don samun kyakkyawar shayarwa ki kiyaye: banda bada nono akwance komi gajiya, komi dare ki tashi zauna kisashi a cinya haka zai hanashi kumburin ciki, sannan idan yasha kika ga alamun kamar ya isa ya koshi to ki dauke kisashi akafadarki ki rika shafa bayansa zuwa can zakiji yai gyatsa wannan alama ce ta ya koshi kuma nono ya tsirga masa ciki kya iya mayar dashi ki kwantar.
Inko bakiji yai gyatsa ba tohfa duk dadewar da kikai kisani nono bai ishesa ba don haka ki maida shi ya kara.
Wannan bayanin ba ga mata ba kadai kaima amatsayinka na Maigida Käna da rawar da zaka taka don ganin kun kula da jaririnku. Sannan a tabbatar ana samarwa da mahaifiyar isashshen abinci mai inganci domin lafiyarta itace lafiyar jaririn.
Fatan bayanin ya ilmantar. Idan ya ilmantar to kayi Mana sharing zuwa gaba.
ADAMSY TRADITIONAL MEDICINE
WhatsApp/Viber: 08036066553
Telegram/Wechat: 08093651535
Imo Chat: 08051115383
Twitter/BBM:@Adamsymedicine
Instagram: @Adamsymedicne
Website: Adamsymedicine.blogspot.com
EMAIL: adamsymedicine@gmail.com

Comments
Post a Comment