ABUBUWA 7 DA KA IYA LALATAMAKA KODA
1. Jan nama - Jan nama na dauke da kwayoyin gina jiki wato Protein da yawan gaske. Duk da cewa jiki na bukatar wannan domin gina jiki, yawan Protein a jiki na wahalar da kodar wanda zai sa shi gajiya da wuri. 2. Man Shanu - Man Shanu na dauke da mai wanda ka iya haddasa ciwon zuciya. Gidauniyar Koda ta kasa ta bayyana cewa ciwon zuciya babban barazana ne ga lafiyar koda 3. Gyada - Gyada na dauke da sinadarin Oxalate, shi ke haddasa duwatsun da ke tsirowa idan koda ya kusa lalacewa 4. Giya da kayan maye - Giya da barasa na daya daga cikin abubuwan da ke saurin lalata kodar dan Adam saboda ta kan sauya yanayin jikin mutum cikin kankanin lokaci. 5. Gishiri - Asali, gishiri na da amfani da jikin dan Adam. Yana rage hawan jini, yana tafiyar da ruwan jiki, kuma yana taimakawa jijiyoyin. Amma idan yayi yawa, zai iya lalata kodar mutum. 6. Lemun kwalba mai gas - Lemun kwalban da aka cushe da iskar gas. Yawan shan su na iya ynjo tsi